Sunday, April 5, 2026
HomeLabaraiAn karkatar da Naira Bilyan 71.2 daga cikin Bilyan 100 na bashin...

An karkatar da Naira Bilyan 71.2 daga cikin Bilyan 100 na bashin dalibai a Nijeriya – Hukumar ICPC

Hukumar ta ICPC da kan yaki cin hanci a tsakanin jami’an gwamnati wato ICPC ta bayyana cewa Naira biliyan 28.8 ne kawai aka rabawa dalibai a manyan makarantun gaba da sakandare maimakon Naira biliyan 100 da aka rabawa makarantun.

Hukumar ta ce binciken farko da ta gudanar ya gano cewa hukumomin jami’o’i daban-daban sun karkatar da adadin kudaden da basu kasa Naira biliyan 71.2 ba, kamar yadda jaridar Dailytrust ta ruwaito.

Kakakin hukumar, Demola Bakare, ya shaidawa manema labarai a Abuja cewa an gayyaci manyan masu ruwa da tsaki da suka hada da darakta janar na ofishin kasafin kudi da kuma akanta janar na kasa.

Haka kuma Bakare ya ce an gayyaci manyan jami’ai daga bankin CBN da kuma babban daraktan shirin bada lamuni na dalibbai wato NELFUND domin su ba da bayanai kan lamarin.

Ukashatu Ibrahim Wakili
Ukashatu Ibrahim Wakilihttps://dclhausa.com
Ukashatu Wakili, Mataimakin Manajan Edita kuma Mai Kula da Shirin Koyon Sanin Makamar Aiki ne a DCL Hausa. A matsayinsa na ƙwararren ɗan jarida yana tsara ayyukan rediyo da kafafen sada zumunta, fassarar labarai, da tabbatar da sahihancin bayanai. Yana jagorantar shirin horaswa ga masu koyon aiki tare da kula da ingancin rubuce-rubuce da shirye-shiryen gidan jaridar.
RELATED ARTICLES

1 COMMENT

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata