Wednesday, April 8, 2026
HomeUncategorizedAn rage shigo da tataccen mai daga Turai bayan bude matatar man...

An rage shigo da tataccen mai daga Turai bayan bude matatar man Dangote a Nijeriya – OPEC

Kungiyar kasashen dake fitar da arzikin mai ta OPEC , ta ce fara tace man fetur da dangogin sa da matatar mai ta Dangote ta fara ya rage yawan shigo da tataccen mai daga Turai.

Ta cikin rahoton wata -wata na kasuwar mai da dangogin sa da aka wallafa a ranar 15 ga Janairun 2025, kungiyar ta OPEC , ta ce samar da wadataccen man daga matatar ta Dangote ya sa tilas yanzu wasu kamfanonin su nemi kasuwa a wasu guraren.
Haka zalika rahoton ya ce shigowar matatar a kasuwar duniya da sauye -sauyen da ta samar zai kawo gagarumin kalubale ga kasuwar mai ta duniya
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata