Sunday, April 5, 2026
HomeLabaraiAn rufe jami'ar FUDMA bayan zanga-zangar dalibai

An rufe jami’ar FUDMA bayan zanga-zangar dalibai

 

Hukumomi a Jami’ar Tarayya da ke karamar hukumar Dutsinma a jihar Katsina ta rufe jami’ar biyo bayan zanga-zangar dalibai sanadiyyar halbe wani dalibin jami’ar.

Rahotanni sun ce jami’an rundunar hadin gwiwa ta Civilian Joint Task Force da ke aiki a yankin sun halbi dalibai biyu, lamarin da ya yi sanadiyyar rasuwar daya daga ciki.

Wani ganau ya shaidawa Jaridar PUNCH cewa daliban masu zanga-zanga sun tare babbar hanyar Dutsinma zuwa Katsina tare da kona tayoyi.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata