Sunday, April 5, 2026
HomeSiyasaAn saka ranar 14 ga Afrilu don yanke hukunci kan bukatar ba...

An saka ranar 14 ga Afrilu don yanke hukunci kan bukatar ba da belin El-Rufai

Kotun Tarayya da ke Kaduna ta sanya ranar 14 ga watan Afrilu, 2026 domin yanke hukunci kan bukatar beli da tsohon gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai ya gabatar.

A yau Laraba ne lauyoyin El-Rufa’i wanda ake kara da kuma masu gabatar da kara wato ICPC suka gabatar da hujjojinsu a gaban kotun da ke Kaduna domin duba batun bukatar ba da tsohon gwamnan na jihar Kaduna beli.

Babban lauyan masu kare El-Rufai, Adewole Iyamu, ya bayyana cewa suna da kwarin gwiwar samun sakamako mai kyau, yana mai cewa sun gabatar da dukkan hujjojinsu yadda ya kamata a gaban kotu.

Iyamu ya tabbatar da cewa an gabatar da bukatar belin a hukumance, kuma bangaren masu kara sun mayar da martani akan bukatar.

Haka kuma, ya ce ana sa ran El-Rufai zai gurfana a gaban Kotun Tarayya da ke Abuja a ranar 10 ga watan Afrilu kan wata kara daban da Hukumar Tsaron Farin Kaya (DSS) ta shigar.

A cewarsa, bangaren wanda ake kara sun kammala dukkan shirye-shiryen da suka dace domin sauraron karar ranar 10 ga Afrilu, inda ya ce sun riga sun shigar da dukkan takardun da ake bukata.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata