Monday, April 6, 2026
HomeBabban LabarinmuAn samu Gwamna a Nijeriya da ke yekuwar shugaban kasa da gwamnoni...

An samu Gwamna a Nijeriya da ke yekuwar shugaban kasa da gwamnoni su rika yin wa’adin mulki daya na shekaru 6 a bisa mulki

Gwamna Seyi Makinde na Jihar Oyo ya yi kira da a sauya tsarin mulki domin bai wa masu mukaman siyasa da aka zaba a matakai daban-daban na gwamnati damar yin wa’adi guda na shekaru biyar ko shida kacal, maimakon wa’adin biyu na shekaru hudu-hudu da ake yi a yanzu.

Gwamnan ya bayyana hakan ne a lokacin da wasu Musulmai da suka hada da malamai, sarakunan gargajiya da masu rike da mukaman siyasa suka kai masa ziyara a gidansa da ke Ikolaba, Ibadan, bayan kammala sallar layya da aka gudanar a filin idi na Agodi, Ibadan.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata