Sunday, April 5, 2026
HomeBabban LabarinmuAn samu hargitsi a taron APC a lokacin da Ganduje ya ayyana...

An samu hargitsi a taron APC a lokacin da Ganduje ya ayyana goyon bayan tazarcen Shugaba Tinubu ba tare da Kasshim Shettima ba

An samu rikici a taron jiga-jigan jam’iyyar APC na Arewa maso Gabas a ranar Lahadi, bayan da Mataimakin Shugaban Jam’iyyar na Kasa a yankin, Comr Mustapha Salihu, ya kasa ambato sunan Mataimakin Shugaban Kasa Kashim Shettima yayin da yake bayyana goyon bayan sake tsayawa takarar Shugaba Bola Tinubu a karo na biyu.

An gudanar da taron ne a Jihar Gombe, inda kusan dukkan ministoci, ‘yan majalisa da gwamnonin jam’iyyar daga yankin suka halarta kamar yadda jaridar Daily Trust ta rawaito.

Ukashatu Ibrahim Wakili
Ukashatu Ibrahim Wakilihttps://dclhausa.com
Ukashatu Wakili, Mataimakin Manajan Edita kuma Mai Kula da Shirin Koyon Sanin Makamar Aiki ne a DCL Hausa. A matsayinsa na ƙwararren ɗan jarida yana tsara ayyukan rediyo da kafafen sada zumunta, fassarar labarai, da tabbatar da sahihancin bayanai. Yana jagorantar shirin horaswa ga masu koyon aiki tare da kula da ingancin rubuce-rubuce da shirye-shiryen gidan jaridar.
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata