Sunday, April 5, 2026
HomeLabaraiAn shiga firgici yayin da jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna ya sauka...

An shiga firgici yayin da jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna ya sauka daga kan hanyarsa 

Rahotanni da gidan talabijin na Channels ya tattaro sun nuna cewa wani jirgin ƙasa da ke tafiya daga Abuja zuwa Kaduna ya fadi daga kan layi a safiyar Talata, lamarin da ya jefa fasinjoji cikin tashin hankali da firgici.

Shaidun gani da ido daga cikin jirgin sun bayyana cewa mutane sun ruga neman dauki daga jama’a cike da rudewa.

Har yanzu ba a tabbatar da musabbabin hatsarin ba, haka kuma babu tabbacin ko an sami raunuka ko asarar rayuka.

Hukumar tsaro ta ce an tura dakarun soji zuwa wurin domin taimaka wa wajen fitar da fasinjojin da suka makale.

RELATED ARTICLES

1 COMMENT

  1. Comment:Allah gamu gareka, wai kam talaka ina zai sa kansa ne? Ko ina ba dadi, hanyoyin mota ba kyau na jirgin kasa ma haka.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata