Monday, April 6, 2026
HomeBabban LabarinmuAn soke zaben June 12 ne saboda bashin Naira bilyan 45 da...

An soke zaben June 12 ne saboda bashin Naira bilyan 45 da MKO Abiola yake bin gwamnatin tarayya – Sule Lamido

Tsohon gwamnan jihar Jigawa, Sule Lamido, ya alakanta soke zaben shugaban kasa da aka gudanar a ranar 12 ga watan Yunin 1993 da Marigayi MKO Abiola ya lashe da bashin Naira bilyan 45 na kwangila da Abiola yake bin gwamnatin mulkin soja ta Marigayi Janar Murtala Mohammed.

A cewar Lamido, an ki biyan Abiola bashin bayan rasuwar Janar Mohammed, kuma a lokacin da Abiola ya lashe zaben shugaban kasa, sai aka soke shi saboda fargabar cewa idan aka rantsar da shi a matsayin shugaban kasa, Abiola zai biyan kansa bashin, lamarin da ka iya durkusar da kasar a lokacin.

Sule Lamido ya bayyana hakan ne a ranar Talata a Abuja a lokacin kaddamar da littafin tarihin rayuwarsa mai suna ‘Being True to Myself’.

Ukashatu Ibrahim Wakili
Ukashatu Ibrahim Wakilihttps://dclhausa.com
Ukashatu Wakili, Mataimakin Manajan Edita kuma Mai Kula da Shirin Koyon Sanin Makamar Aiki ne a DCL Hausa. A matsayinsa na ƙwararren ɗan jarida yana tsara ayyukan rediyo da kafafen sada zumunta, fassarar labarai, da tabbatar da sahihancin bayanai. Yana jagorantar shirin horaswa ga masu koyon aiki tare da kula da ingancin rubuce-rubuce da shirye-shiryen gidan jaridar.
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata