Monday, April 6, 2026
HomeUncategorizedAn yi ajalin mata 50 a Nijeriya cikin watanni uku in ji...

An yi ajalin mata 50 a Nijeriya cikin watanni uku in ji wani rahoton da jaridar Daily Trust ta wallafa

Wata kwararriyar mai bincike kan harkokin da suka shafi mata Ololade Alayi ta koka kan yadda ake samun karuwar ajalin mata a Nijeriya, inda bincikenta ya gano cewa tsakanin watannin Janairu da Fabrairun 2025 kadai, an yi ajalin mata 34, a watan Maris kuwa aka samu 16 a Nijeriya.

Ms. Ololade ta bayyana cewa, duk da cewa adadin da aka ambata ya shafi watan Janairu da Fabrairu, DOHS Foundation ta riga ta samu rahoton ajalin mata guda uku a watan Maris, wadanda suka faru kafin ko a ranar 8 ga Maris, ranar da aka gudanar da bikin makon mata na Duniya.

Ta kara da cewa, a watan Janairu an yi ajalin mata guda 17, yayin da a watan Fabrairu aka samu guda 15, Kuma adadin na ci gaba da karuwa, a cewar Ololade, wannan karuwar mummunan lamari kan mata na nuna cewa a duk kwana biyu, ana ajalin mace guda a Najeriya.

A cikin rahoton Hukumar Amnesty International, na shekarar 2024, mata da ‘yan mata guda 149 ne aka yi ajalisu Najeriya. A matakin duniya kuwa, rahoton Hukumar Mata ta Majalisar Dinkin Duniya na shekarar 2024 ya bayyana cewa a shekarar 2023, mata da ‘yan mata guda 85,000 aka kawar, wanda kasha 60% na wadannan abin ya shafa an yi su ne da hannun abokan zama ko ‘yan uwa.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata