Sunday, April 5, 2026
HomeBabban LabarinmuAna bin 'yan Nijeriya bashin Naira bilyan 54 na kudin lantarkin da...

Ana bin ‘yan Nijeriya bashin Naira bilyan 54 na kudin lantarkin da suka sha a watan Fabrairun wannan shekara, 2025

Wani rahoto da jaridar Punch ta wallafa ya nuna cewa ana bin ‘yan Nijeriya da ke amfani da wutar lantarki bashin kudin da suka kai sama da Naira bilyan 54.

Wannan bashin na wutar lantarkin da suka sha ne a watan Fabrairu na wannan shekarar 2025, a cewar rahoton hukumar kula da lantarki ta Nijeriya NERC.

A cikin takardar bayanai da ta fitar na watan Fabrairu, NERC ta bayyana cewa kamfanonin rarraba lantarki na Discos 12 sun samu an biya su kudin lantarki Naira bilyan 191.75 daga cikin jimillar biyan kudin wutar lantarki na Naira bilyan 245.93.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata