Rahotanni sun bayyana cewa ana bincikar tsohon gwamnan ɗaya daga jihohin kudu bisa zargin cewa yana da alaƙa da wasu jami’an soji 16 da aka tsare bisa tuhumar shirya juyin mulki a Najeriya.
Majiyar Daily Trust ta ce akwai zargin cewa tsohon gwamnan ya taimaka wajen ɗaukar nauyin shirin da aka ce an tsara gudanar da shi a ranar 25 ga watan Oktoba.
A ƙarshen makon da ya gabata, ne kafafen labarai Sahara Reporters da Premium Times suka ruwaito cewa jami’an 16 da Hedikwatar Tsaron ƙasa ta tabbatar da kama su bisa saba ƙa’idojin aiki, ana bincikensu ne kan zargin yunƙurin kifar da gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu.
Wasu daga cikin waɗanda ake tsare da su ciki har da Brigadier-General, Colonel, da wasu ƙananan jami’ai, an ce suna aiki a Ofishin Mai Bai wa Shugaban Ƙasa Shawara kan Tsaro.
Saidai rundunar sojin Nijeriyar ta bakin mai magana da yawunta Birgediya Janar Tukur Gusau ta karyata rahotannin da ake alakantawa da Shirin jami’an na kifar da gwamnatin dimokradiyya a kasar.
