Sunday, April 5, 2026
HomeBabban LabarinmuAna zargin wani matashi ya yi ajalin mahaifinsa a Jigawa

Ana zargin wani matashi ya yi ajalin mahaifinsa a Jigawa

Rundunar ‘yan sanda ta kama wani matashi dan shekara 20 mai suna Muhammad Salisu da ake zargin ya yi ajalin mahaifinsa Salisu Abubakar inda ya daddatsa shi da adda a karamar hukumar Gwaram ta jihar Jigawa.

Da yake tabbatar da faruwar lamarin a wata sanarwa da aka rabawa manema labarai a Dutse, a ranar Litinin, jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, Shi’isu Adam, ya ce lamarin ya faru ne da misalin karfe 10 na safe a unguwar Bakin Kasuwa da ke yankin Sara.

A cewar kakakin, wanda ake zargin ya yi amfani da adda, inda ya yi wa mahaifinsa munanan raunuka a kafada, wuyansa, da kuma kirji.

Nan take aka garzaya da shi babban asibiti da ke Birnin Kudu, sai dai a can ne Likita ya tabbatar da mutuwarsa.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata