DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Saturday, April 11, 2026
HomeUncategorizedAna zargin wata mata da yin ajalin mijinta ana shirye-shiryen bikin sunan...

Ana zargin wata mata da yin ajalin mijinta ana shirye-shiryen bikin sunan ɗansa

 

‘Yan sanda

An kama wata mata mai suna Fatima Dzuma ‘yar kimanin shekaru 27 bisa zargin ta da ajalin mijinta Baba Aliyu mai shekaru 25 a jihar Neja.

Lamarin dai ya faru ne a kauyen Lafiyagi Dzwafu da ke karamar hukumar Katcha ta jihar, a lokacin da ake shirye shiryen bikin nadin sunan dansa da matarsa ta farko ta haifa masa.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Neja, Abiodun Wasiu, ya ce an kama Fatima ne bayan an gano gawar mijinta a wani daji da ke kusa da gidansu, kwanaki uku bayan an nemeshi an rasa.

A wata sanarwa da ya fitar a ranar Juma’a, kakakin ‘yan sandan ya ce wadda ake zargin ta amsa laifin da ake tuhumar ta da shi, inda ta ce a lokacin da mijin ta yake barci ta halaka shi, sannan ta daure shi da igiya kafin ta jefar da gawar a cikin daji.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata