Jam’iyyar APC reshen jihar Kebbi ta sanar da dawo da Kabir Sani-Giant, mai ba Gwamna Nasir Idris shawara kan harkokin wutar lantarki da siyasa, zuwa kujerarsa nan take.
An dakatar da Kabir Sani-Giant a ranar 28 ga Fabrairu, 2025, bisa zargin kawo maciji fadar gwamnati a ranar 8 ga watan nan, da nufin tsoratar da manyan baki, jami’an gwamnati.
A wata sanarwa da Shugaban APC na Jihar Kebbi, Muhammad Kana-Zuru, ya fitar a ranar Litinin daga Birnin Kebbi, ya bayyana cewa kwamitin gudanarwa na jiha ya karanta kuma ya yi la’akari da takardar afuwar da Sani-Giant ya rubuta, kuma ya yanke shawarar janye dakatarwar da aka yi masa.

Comment:masha allah haka mukeso a dunga yafiya
I am not sure where you’re getting your information, but great topic.
I needs to spend some time learning more or understanding more.
Thanks for fantastic information I was looking for this information for my mission.