DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Sunday, April 12, 2026
HomeUncategorizedAtiku Abubakar ya musanta karbar tallafin kudin kamfe daga Gwamna Sanwo Olu...

Atiku Abubakar ya musanta karbar tallafin kudin kamfe daga Gwamna Sanwo Olu na jihar Lagos a lokacin zaben 2023

Atiku Abubakar

Tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar musanta ikirarin da ake na cewa gwamnan jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu ya bashi tallafin kudi na yakin neman zabe a zaben shugaban kasa da ya gabata.

A wata sanarwa da mai magana da yawun sa Paul Ibe ya fitar, ofishin yada labarai na Atiku ya karyata rahotannin da ke nuni da cewa Sanwo-Olu, ta hannun Ms. Aisha Achimugu, ya bai wa tsohon mataimakin shugaban kasa kudi da ake zargin mallakar jihar Legas ne, abinda ya kira makircin ‘yan siyasa da suka kulla.

A farkon makon da ya gabata ne jaridar PREMIUM TIMES ta ruwaito cewa ana binciken Ms Achimugu kan zargin karkatar da kudade da dama.

Hukumar EFCC mai yaki da cin hani da rashawa a Nijeriya na ci gaba da binciken matar da ake zargi.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata