Atiku ya jinjinawa masu zanga-zanga, ya kuma nemi Tinubu da ya saurari al’umma
Tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar ya jinjinawa ‘yan Najeriya da suka fito kan tituna domin nuna adawa da gwamnatin babban abokin hamayyarsa a zaben da ya gabata.
A wata sanarwa da ya fitar a ranar Juma’a, Atiku ya yabawa ‘yan Najeriya bisa jajircewar da suka nuna yayin da ya yi Allah wadai da wayan da suka yi sace sace a yayin zanga-zanga a wasu jihohin.
Ya kuma bukaci jami’an tsaro da su lura da yadda suke gudanar da ayyukan su,su kuma daina muzgunawa ‘yan jarida da masu zanga-zanga da harbe harbe.
Tsohon mataimakin shugaban kasar ya bukaci gwamnatin Tinubu da ta saurari mutane tayi abin da al’umma suke so
Yace fara zanga-zangar da jama’a suka yi a fadin Nijeriya ya nuna rashin amincewa da manufofin gwamnati, tare da ci gaba da tattaunawa mai mahimmanci game da shugabanci nagari a cikin al’ummarmu.
“Ina kira ga masu zanga-zangar da su yi cikin lumana tare da yin kira ga ‘yan Najeriya da su kara nuna goyon baya da goyon bayan zanga-zangar lumana ta #EndBadGovernance. Wannan wani muhimmin lokaci ne da za a ji muryarmu ta gama gari, kuma dole ne a yi shi cikin mutunci da mutunta doka.
“Ina kuma kira ga ‘yan sanda da su kara kaimi wajen tafiyar da wadannan masu zanga-zangar. Kisan gillar da jami’an tsaro ke yi wa ‘yan kasa ba gaira ba dalili abu ne da ba za a amince da shi ba. Dole ne ‘yan sanda su guji cin zarafin ‘yan jarida da ke ba da rahoton zanga-zanga. Ya zama wajibi hukumomin tsaro su yi taka-tsantsan wajen tabbatar da doka da oda.

