Sunday, April 5, 2026
HomeBabban LabarinmuAtiku ya jinkirta yankar katin ADC, bayan rade-radin zawarcin Jonathan da aka...

Atiku ya jinkirta yankar katin ADC, bayan rade-radin zawarcin Jonathan da aka ce jam’iyyar na yi

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, ya dakatar da shirin karbar katin zama mamba na jam’iyyar ADC, yayin da ake rade-radin tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan na iya shiga takarar shugaban kasa a 2027 tare da neman goyon bayan jam’iyyar.

Atiku, wanda ya fice daga PDP bayan rikice-rikicen cikin gida, ya shirya karbar katin a mazabarsa ta Jada, Adamawa, a ranar 6 ga Agusta, amma an dage taron ba tare da saka sabon lokaci ba.

Shugaban ADC na Adamawa, Shehu Yohana, ya ce Atiku na jiran wasu gwamnoni daga APC su koma ADC kafin a gudanar da muhimmin taron.

Sai dai jaridar Punch ta ce wasu jiga-jigan ADC sun nuna jinkirin na iya zama saboda takaddama tsakanin Atiku da tsohon dan takarar shugaban kasa na LP, Peter Obi, wanda ake zargin ya mamaye tsarin jam’iyyar a Kudu.

Sun kuma yi hasashen cewa idan lamarin bai tafi yadda Atiku ke so ba, zai iya komawa jam’iyyar SDP.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata