DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Monday, April 13, 2026
HomeKetareAustralia ta nada mace shugabar sojojin ƙasar a karon farko

Australia ta nada mace shugabar sojojin ƙasar a karon farko

Australia ta sanar da cewa za a fara samun mace a matsayin shugabar rundunar sojin ƙasa a karon farko cikin tarihin shekaru 125 na rundunar, a wani bangare na sauye-sauyen shugabanci da ake yi a rundunar tsaron ƙasar.

Laftanar Janar Susan Coyle, wadda a halin yanzu ke rike da mukamin shugabar bangaren dabaru da hadin gwiwar ayyukan soja, za ta karbi ragamar shugabancin rundunar daga watan Yuli, kamar yadda gwamnati ta bayyana. Za ta maye gurbin Laftanar Janar Simon Stuart, wanda ya fara rike wannan mukami tun watan Yuli na shekarar 2022.

Coyle ta shafe kusan shekaru arba’in tana aiki a rundunar soja, inda ta rike manyan mukamai na jagoranci, ciki har da shiga manyan ayyuka a Afghanistan da kuma yankin Gabas ta Tsakiya.

Nadin nata ya zo ne a daidai lokacin da rundunar sojin Australia ke kokarin kara yawan mata a cikinta, yayin da take fuskantar zarge-zargen cin zarafi da wariya da ake cewa sun dade suna faruwa a cikin rundunar.

Firaministan Australia, Anthony Albanese, ya bayyana cewa daga watan Yuli, rundunar za ta samu mace ta farko a matsayin shugabarta a tarihin ta na shekaru 125.

Ministan tsaro, Richard Marles, ya bayyana wannan nadin a matsayin wani muhimmin tarihi, yana mai cewa nasarar da Coyle ta samu za ta zama abin koyi ga mata da ke aikin soja a yanzu da kuma wadanda ke shirin shiga a nan gaba.

Ya kara da cewa, kamar yadda Coyle ta bayyana masa, mutum ba zai iya zama abin da bai taba gani ba — ma’ana ganin mace a irin wannan matsayi zai karfafa gwiwar wasu mata su taka irin wannan hanya.

A halin yanzu, rundunar sojin Australia na cikin wani babban sauyi, inda take kara karfafa kanta da sabbin kayan yaki irin su makamai masu nisan zango, jirage marasa matuka da kuma sabbin fasahohin zamani.

Coyle, mai shekaru 55, ta jaddada cewa tana da kwarewa a fannoni da dama ciki har da yaki ta yanar gizo, tana mai cewa wannan gogewa na ba ta cikakken tushe wajen daukar wannan babban nauyi na jagoranci da aka dora mata.

A kididdiga kuwa, mata na da kusan kashi 21 cikin 100 na rundunar tsaron Australia, yayin da kashi 18.5 cikin 100 ke rike da manyan mukaman jagoranci. Rundunar ta sa burin kai kashi 25 cikin 100 na mata nan da shekarar 2030.

A watan Oktoban da ya gabata, an shigar da karar hadin gwiwa a kotu kan rundunar, inda ake zarginta da gazawa wajen kare dubban mata daga fyade, cin zarafi da wariya.

A gefe guda kuma, gwamnati ta nada Vice Admiral Mark Hammond, wanda ke jagorantar rundunar ruwa a yanzu, a matsayin sabon shugaban rundunar tsaron ƙasar baki daya, inda zai maye gurbin Admiral David Johnston.

Shi kuwa mataimakin shugaban rundunar ruwan na yanzu, Rear Admiral Matthew Buckley, shi ne zai karbi ragamar jagorancin rundunar ruwan daga hannun Hammond.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata