Ba da jimawa ba za a kawo karshen shugaban ‘yan bindiga, Bello Turji- Gwamnatin Zamfara
Gwamnan jihar Zamfara ya yi imanin cewa nan ba da jimawa ba za a kawo karshen ta’addancin da fitaccen bindigar nan mai suna Bello Turji ya yi wa jihar da wasu sauran jihohin dake kusa dasu.
Gwamna Lawal kuma yaba da tabbacin cewa nan ba da jimawa ba za a kama ko kuma a kawar da shi.
Gwamnan ya bayyana haka ne a ranar Litinin a gidan talabijin na Channels cikin shirin Politics today lokacin da aka tambaye shi game da yiwuwar dakatar da wannan dan bindigar.
Yace tare da hadin gwiwar da gwamnatocin jihohin ke dashi tare da hukumomin tsaro yana da tabbacin cewa nan bada jimawa ba za a kawo karshen Bello Turji a cewarsa batune na dan lokaci
Kalaman gwamnan na zuwa ne kwanaki kadan bayan da sojoji suka samu gagarumar nasara a kan ‘yan bindiga, inda suka halaka shugaban ‘yan fashin da ake nema ruwa a jallo, Halilu Sububu, wanda ya addabi al’umma a Zamfara, Sakkwato da sauran sassan Arewa maso Yamma.
Yace wannan yana da matukar muhimmanci wajen kawo karshen ayyukan ta’addanci gaba daya,
“Idan za mu iya ci gaba da wannan matsin lamba a cikin makonni biyu zuwa wata daya masu zuwa, ku yarda da ni, cewa batun ‘yan bindiga za a iya kau dashi.

