Shugaban jam’iyyar riko na jam’iyyar ADC David Mark, yace sabuwar hadakar jam’iyyar bata da wani dan gaban goshi da take shirin tsayarwa takarar shugaban kasa a zaben 2027 dake tafe a Nijeriya.
Jaridar Punch ta rawaito cewa rahotanni daban daban sun ce tsofaffin yan takarar shugaban kasa a zaben 2023 Atiku Abubakar da Peter Obi, tare da tsohon ministan sufuri Rotmi Amechi sune kan gaba wajen a nuna sha’awar tikitin takarar shugabancin kasar a karkashin jam’iyyar ta ADC.
Duk da yake akwai zarge-zarge da tsohon dan takarar shugaban kasa a zaben 2023 karkashin jam’iyyar ta ADC Dumebi Kachikwu ya yi ga shugabancin rikon da Sanata David Mark ke yi, cewa yana nuna fifiko ga bangaren Atiku Abubakar.
Sai dai Mark yaba ‘yan Nigeria yakinin yin aiki bisa gaskiya da rikon amana da kuma tafiyar shugabancinsa bisa adalci ga kowa da kowa a fafitikar da suke ta karbe mulki a hannun APC.
