Rundunar ‘yansandan Najeriya ta ce har yanzu ba ta samu takardar umarnin kotu kan hana amfani da bakin gilashin mota ba.
Mai magana da yawun rundunar CSP Benjamin Hundeyin ne ya bayyana haka yayin da yake martani kan rahotannin da ke cewa kotu ta bayar da umarnin dakatar da matakin nasu.
Tun da fari dai wata babbar kotun tarayya ce ta bayar da umarnin dakatarwar, har zuwa lokacin da za a kammala shari’a kan karar da aka shigar, kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.
Sai dai a shafin sa na X, Hundeyin ya ce har zuwa wannan lokaci ba su karbi wata sanarwa ko takarda a hukumance da ke tabbatar da umarnin ba.
