DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Monday, April 13, 2026
HomeKetareBa na jin tsoron Trump - Paparoma Leo XIV

Ba na jin tsoron Trump – Paparoma Leo XIV

Shugaban cocin Katolika na duniya, Paparoma Leo XIV, ya bayyana cewa ba ya jin tsoron gwamnatin Donald Trump, yana mai cewa zai ci gaba da bayyana sakon zaman lafiya na littafin Injila, bayan shugaban Amurka caccake shi a daren da ya gabata.

Da yake magana da ‘yan jarida a jirgin da ke dauke da shi zuwa birnin Algiers na kasar Algeria a farkon ziyarar kwanaki 10 a Afirka, shugaban cocin ya jaddada cewa cocin ba ta gudanar da siyasa ko manufofin kasashen waje irin yadda gwamnatoci ke yi.

Ya ce ba ya jin tsoron gwamnatin Trump, kuma ba zai daina bayyana sakon Injila da karfi ba, wanda ya ce shi ne abin da aka aiko shi ya yi, tare da jaddada cewa cocin ba ‘yan siyasa ba ne, kuma ba sa kallon harkokin kasashen waje kamar yadda gwamnati ke yi, amma yana da yakinin cewa sakon Injila na zaman lafiya shi ne ginshikin aikinsa.

Wannan martani ya zo ne sa’o’i kadan bayan Donald Trump ya soki shugaban cocin a kafafen sada zumunta da kuma gaban ‘yan jarida, inda ya kira shi da mai rauni a yaki da laifuka, tare da cewa yana da rauni a harkokin kasashen waje, yana kuma zarginsa da nuna goyon baya ga masu ra’ayin siyasa na wani bangare. Wannan suka ta biyo bayan sukar da shugaban cocin ya yi kan barazanar da ke da nasaba da rikicin Iran, inda ya bayyana su a matsayin abin da ba za a amince da shi ba.

Pope Leo XIV, wanda shi ne shugaban cocin Katolika na farko da aka haifa a Amurka, yana rangadi a kasashen Algeria, Cameroon, Angola da Equatorial Guinea, inda ake sa ran ziyarar za ta mayar da hankali kan bukatun nahiyar Afirka. Ya isa birnin Algiers a safiyar Litinin, inda ake sa ran zai gana da shugabannin siyasa.

Shugaban cocin mai shekaru 69, wanda aka zaba a watan Mayun 2025 bayan rasuwar Pope Francis, ya zama daya daga cikin masu karfi wajen kira ga tattaunawa tsakanin kasashe da kuma adawa da yaki a ‘yan makonnin nan. Ya kuma rika ambaton ayar Injila da ke cewa “Masu samar da zaman lafiya su ne masu albarka”, yana mai cewa ba shi da niyyar shiga muhawara kai tsaye da shugaban Amurka.

Ya kara da cewa ba ya son shiga muhawara da Trump, yana mai jaddada cewa abin da ya fi muhimmanci shi ne a ci gaba da neman zaman lafiya da kuma kawo karshen yake-yake.

Jami’an Vatican sun bayyana cewa wannan ziyara ta fi karkata ne ga harkokin addini da hulda, musamman da kasar Algeria mai rinjayen musulmi, tare da karfafa al’ummar Katolika a sassa daban-daban na Afirka.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata