Tuesday, April 7, 2026
HomeUncategorizedBa zaben 2027 ne ya dami Shugaba Tinubu ba a yanzu –...

Ba zaben 2027 ne ya dami Shugaba Tinubu ba a yanzu – Sunday Dare

Shugaba Tinubu

Mai bai wa shugaban kasa shawara na musamman kan harkokin yada labarai Sunday Dare, ya ce shugaba Bola Tinubu bai damu da babban zabe mai zuwa ba, ya mayar da hankali wajen kokarin kawowa ‘yan Nijeriya ci gaba.

A cikin wani bayani da ya wallafa a shafinsa na X, ya ce Tinubu ya fi damuwa da yadda sauye-sauyen da yake yi za su kawo sauyi mai kyau ga ‘yan kasar.

Dare ya ce, an ga yadda asusun Nijeriya ya karu saboda tsarin tattalin arziki, kuma al’ummar kasar sun ga ga yadda farashin kayayyaki yake kara sauka duk ta dalilin sabbin tsare-tsaren da ake na tattalin arzikin kasar.

Ya ce a ganinsa, ba zabe mai zuwa ne abinda ke gaban shugaban kasar a halin yanzu, ya fi mayar da hankali kan inganta rayuwar ‘yan Nijeriya.

Dare ya bayyana haka ne a daidai lokacin da ake tattaunawa kan hadakar jam’iyyun adawa gabanin babban zabe na 2027.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata