Sale Ado wanda aka fi sani da Sarki, babban da ga kasurgumin dan bindiga Ado Alieru, ya bakunci lahira tare da wasu yan bindigar, kamar yadda rahotanni suka nuna.
Rundunar sojin Nijeriya, a cikin wata sanarwa da ta wallafa a shafinta na Facebook, ta ce dakarun rundunar Operation Fansan Yamma, sun hallaka ‘yan bindiga da dama a kauyen Ƙuncin Kalgo dake Tsafe cikin jihar Zamfara, a farmaki da suka kai ranar Talata 10 ga watan Yunin 2025.
Daga cikin wadanda aka kashe har da wani dan ta’adda da ake kira AUTA, tare da abokansa Abdul Jamilu da Salisu.
Hakama bayanai sun nuna cewa an kawar da karin wasu manyan ‘yan ta’adda guda biyu ciki har da wani mai suna Babayé.
Waɗannan ‘yan ta’addan, a cewar sanarwar sojojin, suna da hannu ga ta’addancin da ake yi a yankin Zamfara.
A wani labarin kuma, sojojin na rundunar Operation Fansan Yamma sun kashe wasu ‘yan ta’adda goma da suka taru a kusa da wata tashar mai da ke kauyen Danjibga.
Ana kyautata zaton ‘yan ta’addan na cikin wadanda suka amsa gayyatar Dogo Sule domin su kai hari.
Sanarwar da daraktan yada labarai na hedkwatar tsaro Manjo Janar MARKUS KANGYE ya sanya wa hannu, ta ce Rundunar sojojin Najeriya na ci gaba da jajircewa wajen kare rayuka da kuma dawo da dawwamammen zaman lafiya a fadin jihar Zamfara da yankin Arewa maso Yamma.
