Wednesday, April 8, 2026
HomeBabban LabarinmuBabban kalubalen da jam’iyyar ADC za ta fuskanta shi ne zaben ɗan...

Babban kalubalen da jam’iyyar ADC za ta fuskanta shi ne zaben ɗan takarar shugaban Kasa – Datti Baba-Ahmad

Ɗan takarar Mataimakin shugaban ƙasa a jam’iyyar LP a zaɓen 2023, Datti Baba-Ahmed, ya bayyana ra’ayinsa kan sabuwar hadakar jam’iyyun adawa da suka ɗora kan jam’iyyar ADC.

A wata hira da aka yi da shi a tashar Arise TV ranar Alhamis, Baba-Ahmed ya ce, wannan hadaka ta ADC na da kamanceceniya da yadda aka haɗa jam’iyyun da suka kafa jam’iyyar APC a 2015, amma ya ce akwai rashin daidaito na tsari a cikin sabuwar haɗakar.

Ya bayyana cewa, a lokacin da aka kafa APC, an riga an ɗauki Tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari a matsayin zababben ɗan takara tun kafin zaɓen fidda gwani.

Sai dai kuma, ita wannan hadakar jam’iyyun da ta haɗa da manyan ‘yan siyasa irin su Atiku Abubakar, Peter Obi, Rotimi Amaechi da sauransu, ba ta bayyana matsayin dan takarar da zai wuce gaba a zaben 2027 ba, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ambato.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata