Monday, April 6, 2026
HomeBabban LabarinmuBabban layin wutar lantarkin Nijeriya ya fadi

Babban layin wutar lantarkin Nijeriya ya fadi

An sake samun faduwar babban layin wutar lantarki “National Grid” na Nijeriya a yau Laraba, lamarin da ya jefa al’umma cikin halin rashin wuta a sassa daban-daban na ƙasar.

Kamfanin rarraba wutar lantarki na Abuja Electricity Distribution Company AEDC ya tabbatar da hakan a wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na X da misalin ƙarfe 11:23 na safe.

Sanarwar da kamfanin ya fitar ta ce rashin wutar da ake fama da shi yanzu ya samo asali ne daga faduwar babban layin, kuma ana kokarin shawo kan matsalar.

Jaridar Punch ta rawaito cewa har zuwa lokacin hada wannan rahoto, ba a bayyana musabbabin faruwar lamarin ba.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata