DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Sunday, April 12, 2026
HomeUncategorizedBarayin daji na hallaka mutanen da suka kama bayan sun karbi kudin...

Barayin daji na hallaka mutanen da suka kama bayan sun karbi kudin fansa – Wasu al’umomin jihar Kaduna

Uba Sani

 

Al’ummar Kauru da ke Kudancin Kaduna sun koka da yadda ‘yan ta’adda ke yin garkuwa da mutanen yankin tare da hallaka su ko da kuwa an biya su kudin fansa.

Kungiyar ci gaban al’ummar karamar hukumar Kauru ta nuna bakin ciki da bacin rai game da harin da aka kai wa al’ummar Surubu a masarautar Kumana, inda aka halaka mutane 3 duk da an biya kudin fansa, don haka suka roki gwamnati da ta samar musu da tsaro mai inganci.

A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun kungiyar, Duniya Achi, ya fitar, ta ce wannan danyen aikin na nuni ne da yadda matsalar tsaro ke kara kamari a karamar hukumarsu.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata