Sunday, April 5, 2026
HomeBabban LabarinmuBayan shafe watanni 23, Ganduje ya ajiye mukamin shugabancin APC

Bayan shafe watanni 23, Ganduje ya ajiye mukamin shugabancin APC

Ta dai tabbata, Abdullahi Umar Ganduje ya yi murabus daga shugabancin jam’iyyar APC ta kasa.

Tsohon Gwamnan jihar Kanon ya ajiye mukamin nasa da yammacin Juma’ar nan, kamar yadda gidan talabijin na TVC ya rawaito. Hakan na zuwa ne ‘yan kwanakin bayan takaddamar da ta biyo bayan babban taron jam’iyyar na shiyyar arewa maso Gabas a Gombe, inda nuna goyon bayan takarar shugaba Tinubu a jam’iyyar a azben 2027 ba tare da ayyana Kashim Shettima a matsayin mataimakinsa ba da gandujen ya yi, ya janyo cece-kuce.

Rahotanni sun ce Dr. Ganduje ya gabatar da uzurin rashin lafiya a matsayin dalilin saukarsa daga kujerar. To amma jaridar Daily Nigerian ta ruwaito cewa jam’iyyar APC ta lallashi Dr. Abdullahi Umar Ganduje da ya ajiye mukamin nasa domin bai wa jam’iyyar damar tsara dabarun tunkarar zaben 2027.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata