Hukumar zaɓe ta ƙasar Uganda ta ayyana Yoweri Museveni a matsayin wanda ya lashe zaɓen shugaban ƙasa, inda samun nasarar ta kai shi ga yin wa’adi na 7 a kan mulki.
A bayanan da hukumar zaɓen ta fitar, Museveni ya yi nasara ne bayan kammala ƙirga ƙuri’u a faɗin ƙasar, lamarin da ya tabbatar da ci gaba da zamansa shugaban ƙasa.
Sai dai jagoran adawa Bobi Wine, ya ƙi amincewa da sakamakon zaɓen, inda ya yi zargin an tafka magudi da karya dokokin zaɓe, tare da cewa sakamakon ba shi al’umma suka tsammaci ji ba.
Rikicin siyasa na iya ƙara tsananta yayin da ‘yan adawa ke neman matakan shari’a da na kasa da kasa domin kalubalantar sakamakon zaɓen, a daidai lokacin da gwamnati ke kira ga kwanciyar hankali da zaman lafiya, kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.
