Sunday, April 5, 2026
HomeSiyasaBukola Saraki zai jagoranci sulhunta 'ya'yan jam'iyyar PDP

Bukola Saraki zai jagoranci sulhunta ‘ya’yan jam’iyyar PDP

Kungiyar gwamnonin jam’iyyar PDP tare da tsoffin gwamnonin jam’iyyar sun nada tsohon Shugaban Majalisar Dattawan Nijeriya Bukola Saraki, a matsayin shugaban kwamitin sulhu mai mambobi bakwai.

Shugaban kungiyar Gwamna Bala Mohammed na Jihar Bauchi, ne ya bayyana hakan yayin da yake ganawa da manema labarai bayan wani muhimmin taro da suka yi da tsoffin gwamnonin jam’iyyar a Abuja.

Gwamna Bala Mohammed ya ce an dora wa wannan kwamiti mai mutane bakwai nauyin sasanta mambobin jam’iyyar da ke cikin sabani kafin babban taron kwamitin zartaswa na kasa NEC na jam’iyyar PDP da aka shirya gudanarwa a ranar 27 ga Mayu, da kuma babban taron jam’iyyar na kasa da ke tafe a watan Agusta.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata