Gwamnatin Burtaniya na nazarin yiwuwar hana yara ‘yan kasa da shekara 16 amfani da kafafen sada zumunta, a wani mataki na rage illar yawan amfani da waya da kuma inganta tsaron yara a yanar gizo.
Firaminista Keir Starmer ya ce suna tattaunawa kan yadda za a takaita amfani da manhajoji kamar Instagram da TikTok, ciki har da saka iyaka ga lokacin amfani da kuma dakile tsarin “scrolling” da ke janyo jaraba.
Gwamnatin ta ce manufar ita ce fahimtar yadda amfani da soshiyal midiya ke shafar bacci, karatu da rayuwar iyali, yayin da ake ci gaba da karɓar ra’ayoyin jama’a kafin yanke hukunci na karshe kan dokar.
