Tuesday, April 7, 2026
HomeUncategorizedCBN ya musanta batun daina karbar tsoffin takardun kudi na Naira a...

CBN ya musanta batun daina karbar tsoffin takardun kudi na Naira a watan Disamba mai zuwa

Sai dai bankin ta hannun mukaddashin daraktan sadarwa Sidi Ali Hakama, ya shawarci ‘yan Nijeriya da su rungumi tsarin hada-hadar kudi na zamani.
Akwai dai wani labari da ake yadawa musamman a kafafen sada zumunta, ana tsoratar da mutane cewa daga ranar 31 GA watan Disamba mai zuwa, za a daina karbar tsoffin takardun kudi na N200, N500 da N1,000.
Idan za a iya tunawa dai, bankin na CBN ya sanar da a cigaba da amfani da tsoffin takardun kudin hade da sabbin kamar yadda kotun koli ta umurta bayan karar da aka shigar a watan Nuwambar 2023.
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata