Sunday, April 5, 2026
HomeLabaraiCire tsoffin 'yan sanda daga daga tsarin Contributory Pension Scheme ya fi...

Cire tsoffin ‘yan sanda daga daga tsarin Contributory Pension Scheme ya fi karfina – IGP Egbetokun

Sufeto Janar na ‘yan sandan Nijeriya, Kayode Egbetokun, ya bayyana cewa ba shi da ikon cire tsofaffin jami’an ‘yan sanda daga tsarin fansho na Contributory Pension Scheme, yana mai jaddada cewa lamarin yana buƙatar matakin dokoki daga majalisar tarayya da sauran hukumomin gwamnati.

A ranar Litinin, tsofaffin ‘yan sanda daga sassa daban-daban sun gudanar da zanga-zanga a majalisar tarayya da kuma hedikwatar rundunar ‘yan sanda a Abuja, suna ƙorafi kan wahalhalu da rashin adalci da suke fuskanta a tsarin fansho da aka sanya su ciki.

IGP Egbetokun, yayin da ya karɓi tawagar shugabannin masu zanga-zangar, ya bayyana damuwarsa da halin da suke ciki.

Ya kuma tabbatar musu da cewa an fara tattaunawa da hukumomin da suka dace domin duba yiwuwar fitar da jami’an ‘yan sanda daga tsarin CPS zuwa tsarin fansho na gargajiya, tare da tabbatar da walwala da mutuncin dukkan masu ritaya.

Ukashatu Ibrahim Wakili
Ukashatu Ibrahim Wakilihttps://dclhausa.com
Ukashatu Wakili, Mataimakin Manajan Edita kuma Mai Kula da Shirin Koyon Sanin Makamar Aiki ne a DCL Hausa. A matsayinsa na ƙwararren ɗan jarida yana tsara ayyukan rediyo da kafafen sada zumunta, fassarar labarai, da tabbatar da sahihancin bayanai. Yana jagorantar shirin horaswa ga masu koyon aiki tare da kula da ingancin rubuce-rubuce da shirye-shiryen gidan jaridar.
RELATED ARTICLES

1 COMMENT

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata