Sunday, April 5, 2026
HomeSiyasaDa gangan na kirkiri labarin kwararowar beraye cikin Villa don kawar da...

Da gangan na kirkiri labarin kwararowar beraye cikin Villa don kawar da hankalin jama’a ga batun rashin lafiyar Buhari – Garba Shehu

Garba Shehu, Tsohon mai magana da yawun Buhari, ya bayyana a littafinsa cewa ya kirkiri labarin beraye sun lalata ofishin shugaban kasa a 2017 don karkatar da hankalin jama’a daga tambayoyin da ake yi kan lafiyar Buhari bayan dawowarsa daga jinya a Birtaniya.

Ya ce labarin ya samo asali ne daga zancen wani kebul da ya lalace a ofishin, wanda aka danganta da beraye.

Labarin ya bazu a duniya, wanda kuma ya taimaka wajen rage matsin lamba kan tuhumar yanayin lafiyar shugaban kasar a wancan lokacin kamar yadda rahoton jaridar Punch ya tabbatar.

RELATED ARTICLES

1 COMMENT

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata