Sunday, April 5, 2026
HomeLabaraiDa yiwuwar a samu ambaliyar ruwa a jihohi 12 na Nijeriya -...

Da yiwuwar a samu ambaliyar ruwa a jihohi 12 na Nijeriya – NEMA

Hukumar ba da agajin gaggawa a Nijeriya NEMA, ta yi kira ga jihohin kasar da su zamo cikin shiri domin tunkarar ambaliyar ruwa da ke iya afkuwa a daminar bana, 2025.

Hukumar ta ce za ta aika tawaga kowace Jiha domin tattataunawa da al’ummar da ake sa ran faruwar ambaliyar domin gargadi da kuma zama cikin shirin ko-ta-kwana.

Darakta Janar ta NEMA, Malama Zubaida Umar ce ta bayyana hakan a wani taron masu ruwa da tsaki da ya gudana a Abuja.

Sai dai, hukumar ta NEMA ba ta ambaci sunayen jihohi da kananan hukumomin da ake sa ran ambaliyar ruwan za ta afku ba.

RELATED ARTICLES

2 COMMENTS

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata