Gamayyar kungiyoyin daliban arewacin Nijeriya sun bayyana janyewarsu daga zanga-zangar da aka shirya yi a fadin kasar nan domin nuna rashin fushinsu da tabarbarewar tattalin arzikin kasarnan.
Shugaban kungiyar daliban jihar Kano ta kasa (NAKS) na majalisar dattijai, Kwamared Jibrin Sani Bello ne ya bayyana hakan a lokacin da yake ganawa da manema labarai a Kano.
Bello ya bayyana cewa janyewar ya samo asali ne na rshin sanin ko su waye masu shirya zanga-zangar.

.jpeg)