Monday, April 6, 2026
HomeBabban LabarinmuDalilin da ya sa har yanzu Shugaba Tinubu bai dawo gida ba...

Dalilin da ya sa har yanzu Shugaba Tinubu bai dawo gida ba – Fadar shugaban kasa

Fadar shugaban Nijeriya ta mayar da martani kan sukar da ake yi wa Shugaba Tinubu, yayin da yake ci gaba da zama a kasar waje a dai dai lokacin da kasar ke fuskantar kalubale da dama.

A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban Bayo Onanuga ya fitar, ya ce shugaban yana ci gaba da gudanar cikin harkokin mulkin Najeriya duk da cewa yana Turai, kuma yana sa ido sosai kan abubuwan da ke faruwa a Najeriya.

Ya kara da cewa shugaban zai dawo Abuja domin ci gaba da aikinsa bayan hutun Esther.

Duk da cewa fadar shugaban kasa ta ce shugaba Tinubu na ziyarar aiki ne a kasar a hukumance, sai dai rahotanni sun ce ya gana da mai bai wa Trump shawara kan harkokin tattalin arziki da tsaro.

Ukashatu Ibrahim Wakili
Ukashatu Ibrahim Wakilihttps://dclhausa.com
Ukashatu Wakili, Mataimakin Manajan Edita kuma Mai Kula da Shirin Koyon Sanin Makamar Aiki ne a DCL Hausa. A matsayinsa na ƙwararren ɗan jarida yana tsara ayyukan rediyo da kafafen sada zumunta, fassarar labarai, da tabbatar da sahihancin bayanai. Yana jagorantar shirin horaswa ga masu koyon aiki tare da kula da ingancin rubuce-rubuce da shirye-shiryen gidan jaridar.
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata