Wednesday, April 8, 2026
HomeUncategorizedDan majalisar dokoki mai wakiltar Kauran Namoda ta kudu a jihar Zamfara...

Dan majalisar dokoki mai wakiltar Kauran Namoda ta kudu a jihar Zamfara Aminu Ibrahim Kasuwar-Daji, ya rasu

Amimu Ibrahim Kasuwar Daji

 Rahotanni sun bayyana cewa dan majalisar ya rasu ne da sanyin safiyar Laraba.

Jam’iyyar APC a jihar Zamfara, ta bayyana alhinin rasuwar dan majalisar.

A wata sanarwa da sakataren yada labaran jam’iyyar a jihar Zamfara Yusuf Idris ya fitar, kwamitin gudanarwa na jam’iyyar na jihar, shuwagabannin jam’iyyar, da magoya bayansa sun yi jimamin rashinsa, inda ya bayyana Hon. Ibrahim Kasuwar-Daji a matsayin mutum mai kwazo, da gaskiya, kuma mai tsoron Allah, wanda ya yi aiki a mazabarsa sossai.

Jam’iyyar ta mika ta’aziyyarta ga iyalan marigayin, al’ummar Kaura Namoda ta Kudu, da ‘yan majalisar dokokin jihar, inda ta yi addu’ar Allah ya ba shi Jannatul Firdaus.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata