Monday, April 6, 2026
HomeUncategorizedDan wasan gaba na Najeriya Ademola Lookman, ya shiga jerin wadanda aka...

Dan wasan gaba na Najeriya Ademola Lookman, ya shiga jerin wadanda aka zaba domin karbar kambun gwarzon dan wasan kwallon kafa na duniya na shekara ta 2024.

Dan wasan Najeriya Ademola Lookman ya shiga cikin jerin fitattun yan  wasan kwallon kafa da su ka hada da Lionel Messi, da Cristiano Ronaldo, da Kylian Mbappé, da kuma Erling Haaland, wadanda aka zaba domin karbar kyautar gwarzon dan wasan kwallon kafa na shekara ta 2024.

Wannan dai wani bangare ne na bukukuwan bada lambar yabo na shekara-shekara na Globe Soccer wanda Hukumar Wasannin Dubai ke shiryawa.

Sanarwar da Globe Soccer Awards su ka wallafa a shafin X a wannan Alhamis, ta ce dan wasan Najeriya Ademola Lookman na cikin wadanda aka zabo domin cin kyautar gwarzon dan wasan kwallon kafa na duniya na 2024.
 

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata