Monday, April 6, 2026
HomeUncategorizedDaukar juna biyu da wuri na kan gaba wajen ajalin mata a...

Daukar juna biyu da wuri na kan gaba wajen ajalin mata a duniya – Rahoton WHO

Hukumar lafiya ta duniya WHO ta yi gargadi game da daukar juna biyu da wuri da ta lura da cewa, hakan yana haddasa mace-macen yara mata masu shekaru 15 zuwa 19 a duniya.

A cikin sabon rahoton da ta fitar, WHO ta bayyana cewa sama da yara mata miliyan 21 ne ke samun juna biyu a kowace shekara a ƙasashe masu karamin karfi, inda kusan rabin waɗannan masu juna biyun basu shirya daukarsa ba.

A cewar hukumar ta lafiya, wannan yana barazana ga inganta kiwon lafiya, yaduwar cututtuka, haihuwar yaran da su da kwarin kashi, da kuma janyo matsaloli a yayin haihuwa.

Ukashatu Ibrahim Wakili
Ukashatu Ibrahim Wakilihttps://dclhausa.com
Ukashatu Wakili, Mataimakin Manajan Edita kuma Mai Kula da Shirin Koyon Sanin Makamar Aiki ne a DCL Hausa. A matsayinsa na ƙwararren ɗan jarida yana tsara ayyukan rediyo da kafafen sada zumunta, fassarar labarai, da tabbatar da sahihancin bayanai. Yana jagorantar shirin horaswa ga masu koyon aiki tare da kula da ingancin rubuce-rubuce da shirye-shiryen gidan jaridar.
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata