DCL Hausa na gayyatar ƙwararru masu jajircewa domin cike guraben aiki na cikakken lokaci (full-time) a ofishinta da ke Kano. Ana neman mutane masu kwarewa, bin ka’ida, da iya aiki cikin lokaci.
Guraben Aiki da ake nema
- Mai Gyaran Bidiyo (Video Editor)
- Mai Rahoto na Kauyuka (Rural Reporter)
Mai Gyaran Bidiyo (Video Editor)
Wuri: Jihar Kano
Nau’in Aiki: Cikakken aiki (Full-Time, a ofis)
Sharuddan Aiki
- Mazaunin Jihar Kano
- Ƙwarewa wajen gyaran bidiyo
- Iya amfani da Adobe Premiere Pro da Canva
- Kwarewar haɗa rahotanni da labaran bidiyo (na gajere da na dogon lokaci)
- Iya aiki cikin lokaci da bin tsarin aiki
- Lokacin zuwa ofis (awanni 8 a rana, kwana 5 a mako)
👉 Cike bayananka/ki nan: https://forms.gle/v8NBCdymW3hzRJeX8
Mai Rahoto na Kauyuka (Rural Reporter)
Wuri: Jihar Kano
Nau’in Aiki: Yin rahoto a karkara
Sharuddan Aiki
- Mazaunin Jihar Kano tare da damar shiga yankunan karkara
- Iya yin rahoto a fili da tattaunawa da jama’a
- Iya ɗaukar bidiyo (wayar hannu ma ta isa)
- Sanin ka’idojin aikin jarida da mutunta al’umma
- Iya aiki cikin lokaci da bin tsarin aiki
👉 Cike bayananka/ki nan: https://forms.gle/FyZDritkPRepk8rd8
Muhimmin Bayani
- Ana buƙatar ladabi, amana, da jajircewa
- Za a tuntubi waɗanda aka tantance kawai
