Nafi’u Bala da ke iƙirarin shugabancin jam’iyyar ADC a Nijeriya ya ce ba za su bar duk wanda ya wuce shekara 50 ya yi takara a jam’iyyar ADC ba.
Nafi’u Bala Gombe ya bayyana haka ne a hirar sa da kafar yaɗa labarai ta BBC Hausa, inda ya ce mafi yawancin mutanen da ke son takara a jam’iyyar sun wuce shekara 80, wasu kuma 70, ko 60, saboda haka ba za su bari ba.
Ya kara da cewa ana ganin kamar ba za su iya ba, saboda a halin yanzu ana bukatar matasa a harkar shugabanci, wannan dalili ya sa za su bai wa masu jini a jika dama a wannan tafiya domin samun nasarar da suke fata a Nijeriya.
