Monday, April 6, 2026
HomeBabban LabarinmuECOWAS ta ayyana dokar ta-baci a ƙasashen yammacin Afirka

ECOWAS ta ayyana dokar ta-baci a ƙasashen yammacin Afirka

ECOWAS ta ayyana dokar ta-baci a ƙasashen yammacin Afirka saboda ƙaruwar juyin Mulki

Kungiyar ECOWAS ta ayyana dokar gaggawa a duk fadin Yammacin Afrika, sakamakon tabarbarewar tsaro da karuwar kalubalen siyasa a kasashen mambobi.

Shugaban Hukumar ECOWAS, Omar Touray, ne ya sanar da hakan a Abuja yayin zaman Majalisar Sulhu da Zaman Lafiya ta ministoci.

Touray ya ce rahotannin da ke gaban ministocin sun nuna cewa mafi yawan kasashen yankin suna cikin matakin haɗari mai tsanani, daga juyin mulki, wahalar sauyin mulki, takura wa zabe, karuwar ayyukan ta’addanci, zuwa matsin lambar ƙasashen waje kan dangantaka da manufofin yankin.

Ya ce abubuwan da suka faru kwanakin nan ciki har da yunkurin juyin mulki a Guinea-Bissau da Jamhuriyar Benin sun tabbatar da bukatar daukar matakin gaggawa.

Ya jaddada cewa zabe ya zama babban abin tayar da hankalin siyasa a yankin, tare da ci gaba da barazanar ‘yan ta’adda, da kuma masu tayar da tarzoma a iyakoki.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata