Wednesday, April 8, 2026
HomeBabban LabarinmuEl-Rufai zai biya diyyar Naira miliyan 900 kan tsare dattawan kabilar Adara...

El-Rufai zai biya diyyar Naira miliyan 900 kan tsare dattawan kabilar Adara ba bisa ka’ida ba a 2019

Kotun tarayya da ke Kaduna ta yanke hukunci kan tsohon gwamnan jihar, Nasir El-Rufai, da wasu mutum biyar, inda ta umarce su su biya Naira miliyan 900 a matsayin diyyar kame da tsare wasu dattawan Adara ba bisa ka’ida ba a 2019.

Mai shari’a Hauwa’u Buhari ce ta yanke hukuncin, tana mai cewa an kama dattawan tara, ciki har da tsohon kwamishina da dan sanda mai ritaya, bisa zargin hannu a kisan sarkin gargajiyar su, Raphael Maiwada Galadima.

An kama su ne bisa umarnin El-Rufai a matsayinsa na dan kasa, ba a matsayin gwamna ba kamar yadda rahoton gidan talabijin na Channels ya ruwaito.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata