Fadar shugaban ƙasa ta musanta zargin tsohon gwamnan Jigawa, Sule Lamido, da cewa Tinubu ya goyi bayan soke zaɓen 12 ga watan Yuni, na 1993.
A wata sanarwa, mai magana da yawun shugaban ƙasa, Bayo Onanuga ya fitar, ya bayyana kalaman Lamido a matsayin kage da yunkurin jirkita tarihi.
Sanarwar ta ce Tinubu ya nuna adawa da soke zaɓen tun yana Sanata, dalili kenan dake nuna yana goyon bayan dimokuraɗiyya da gaskiya.
Sanarwar wadda jaridar Punch ta ambato, ta kuma kare mahaifiyarsa, Hajiya Abibatu Mogaji, daga zargin goyon bayan Babangida, tana mai cewa hakan ba gaskiya ba ne.
Fadar shugaban ƙasa ta jaddada cewa Tinubu ya taka muhimmiyar rawa a NADECO, har ya tsere daga ƙasa, yayin da gidansa a Legas ya fuskanci hari.
