Monday, April 6, 2026
HomeBabban LabarinmuFadar Shugaban Nijeriya ta jefa wa hadakar ADC zazzafan martani kan Jana’izar...

Fadar Shugaban Nijeriya ta jefa wa hadakar ADC zazzafan martani kan Jana’izar Buhari

Fadar shugaban kasa ta musanta zargin jam’iyyar ADC cewa Tinubu da jam’iyyar APC na amfani da rasuwar Buhari don samun karbuwar siyasa, tana mai cewa wannan zargi ba gaskiya ba ne kuma rashin girmamawa ne ga miliyoyin ’yan Najeriya da suka yi alhini.

Mai ba shugaban kasa shawara kan yada labarai, Sunday Dare, ya ce jana’izar Buhari an gudanar da ita cikin cikakken girmamawa da mutunci, tare da halartar shugabanni daga cikin gida da kasashen waje.

Fadar ta kara da cewa gwamnatin Tinubu na ci gaba da aiwatar da manyan ayyuka da suka hada da gyaran tattalin arziki da tallafa wa al’ummar, tare da bukatar ’yan Najeriya su guji rudu da ‘yan siyasa ke kawowa, su mara wa gwamnatin baya a tafiyar da shirin Renewed Hope Agenda da gwamnatin Tinubu ta kafu akai.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata