Kungiyar gwamnonin PDP ta zargi gwamnatin tarayya da aikata danniya, babakere da ɗaukar matakan da suka ce sun saɓa wa dimokuraɗiyya a lokacin zaɓen cike gurbi da aka gudanar a ranar 9 ga Agusta, 2025.
A cewar PDP, an gudanar da zaɓen ne cikin tsangwama, tursasawa, sayen ƙuri’u da kuma tashin hankali, tare da amfani da jami’an tsaro a matsayin kayan aiki wajen murɗe sakamako.
Sai dai fadar shugaban ƙasa ta yi watsi da waɗannan zarge-zargen, tana mai cewa ba su da tushe, illa kawai PDP na jin raɗaɗin shan kaye a filin zabe.
Rahoton da jaridar Punch ta tattaro ya nuna cewa a sakamakon zaɓen, jam’iyyar APC ta samu nasara a kujeru 12, PDP ta lashe kujera ɗaya, APGA ta samu kujeru biyu, yayin da NNPP ta lashe kujera ɗaya.
Sai dai PDP da wasu jam’iyyun adawa sun yi watsi da sakamakon, suna zargin APC da amfani da ƙarfin gwamnati wajen karkatar da zaɓen.
