DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Sunday, April 12, 2026
HomeKetareFaransa ta tabbatar da kasancewar sojojinta a hukumance a jamhuriyar Bénin

Faransa ta tabbatar da kasancewar sojojinta a hukumance a jamhuriyar Bénin

Wasu rahotanni da jaridar Monde Afrique ta ruwaito a shafinta na internet sun bayyana cewa Faransa ta sanar a hukumance kasancewar dakarunta a arewacin Bénin musamman a garuruwan Paraku da Kandi domin horas da sojojin Bénin dan tunkarar yaki da ta’addanci

A cewar wasu majiyoyi, inji jaridar ta Monde Afrique rundunar sojin ta musamman ta Faransar za ta shiga cikin dakarun na Bénin a sirrance domin kaddamar da hare hare a yankunan da ke kan iyaka da kasashen Nijar da Burkina Faso

Daman shugaban gwamnatin mulkin sojan Nijar Janar ABDOURAHAMANE Tiani ya jima yana zargin kasancewar dakarunta na Faransa a cikin Bénin amma hukumomin birnin Cotonou na musantawa8

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata