Farashin danyen mai a kasuwannin duniya ya faɗi ƙasa zuwa dala 95 a kowace ganga, bayan cimma yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin Amurka da Iran.
Rahotan Jaridar Daily Trust ya ce farashin ya ragu da kusan kashi 13 bisa ɗari, inda ya kai tsakanin dala 94 zuwa 95, lamarin da ya zama ɗaya daga cikin manyan sauye-sauyen na lokaci guda a cikin ‘yan shekarun nan.
Saukar farashin ta biyo bayan sanarwar Shugaban Amurka, Donald Trump, na tsagaita hare-hare na tsawon makonni biyu, tare da sharadin bude mashigar Hormuz domin ci gaba da jigilar mai a duniya.
Haka kuma, nau’in man Amurka na West Texas Intermediate ya sauka zuwa kusan dala 95–96, sakamakon raguwar tashin hankalin siyasa da kuma gushewar tsoron katsewar samar da mai.
A baya dai, farashin mai ya haura dala 110 a ganga sakamakon rikicin Gabas ta Tsakiya, amma wannan tsagaita wuta ya dawo da kwarin gwiwa kan ci gaba da zirga-zirgar mai, wanda ya jawo wannan gagarumin sauyi.
Sai dai masana sun yi gargadin cewa kasuwar mai na ci gaba da kasancewa cikin rashin tabbas, domin har yanzu farashin ya fi yadda yake kafin rikicin.
