Sunday, April 5, 2026
HomeUncategorizedFarashin kayan abinci ya fara sauka a sassan Nijeriya

Farashin kayan abinci ya fara sauka a sassan Nijeriya

Har yanzu masara ba ta sauko ba a kasuwar Mai’adua jihar Katsina da ke arewacin Nijeriya, inda ake sai da buhun masarar ₦95,000, yayin da a makon da ya gabata aka sai da ₦90,000 cif .

Sai dai a kasuwannin jihohin Adamawa da Lagos an sai da buhun kan kuɗi ₦90,000 daidai a satin nan, amma a makon jiya farashin ya sha bamban a kasuwannin, inda a jihar Adamawa aka sayar da buhun ₦85,000 a makon da ya shude, sai kasuwar Mile 12 International Market da ke Lagos aka sayar ₦103,000.
To a Kanon Dabo ana sai da buhun masara ₦84,000 a satin na da ke shirin karewa, amma satin da ya wuce ₦87,000 aka sayar da buhunsa, an samu ragin ₦3000 kenan a mako guda.
Farashin masara bai sauya zani ba a kasuwar Giwa jihar Kaduna da aka sayar ₦88,000 a makon da ya gabata, haka ake sayarwa a makon nan.
Ita kuwa Shinkafar Hausa ta fi tsada a kasuwar Giwa jihar Kaduna a wannan satin da ake sayarwa ₦170,000, amma a satin da ya gabata ₦160,000 ne kuɗin buhun Shinkafa a kasuwar.
Sai dai a kasuwar Dawanau jihar Kano farashin bai sauya ba da na makon jiya da aka sai da ₦160,000 daidai.
Haka zalika a kasuwar Mai’adua jihar Katsina farashin buhun Shinkafa ‘yar gida bai canza ba da na satin da ya shuɗe, wanda aka saya kan kuɗi ₦145,000.
A kasuwar Mile 12 International Market Lagos an samu sauƙin ₦5000 kan farashin shinkafa da aka sayar ₦150,000 a makon jiya, yayin da ake sayarwa ₦145,000 a makon nan.
Ita ma dai jihar Adamawa farashin bai sauya tufafi ba a kasuwannin da ake saidawa ₦148,000.
A ɓangaren shinkafar Bature kuwa, ta fi tsada a kasuwar Dawanau jihar Kano da ake sayarwa ₦92,000, haka nan a makon da ya gabata ma shinkafar ta fi tsada a jihar da aka sayar ₦98,000.
Shinkafar waje ta fi sauki a kasuwar Mile 12 International Market da ke jihar Lagos wanda aka sayar ₦75,000 a satin nan, amma a makon jiya ₦76,000 ake sai da buhun.
Ana sayar da Shinkafar waje ₦87,000 a kasuwannin jihohin Katsina da Kaduna da ke arewacin Najeriya a wannan mako, amma dai farashin ya banbanta a makon da ya gabata, inda a kasuwar Giwa jihar Kaduna ake sayarwa ₦85,000, sai Mai’adua jihar Katsina ake sayarwa ₦88,000-₦90,000.
Sai jihar Adamawa ana sayen buhun Shinkafar Bature ₦78,000-₦80,000 a satin nan.
Ga ma’abota cin alala da kosai kuwa ₦200,000 daidai ake sai da buhun farin wake a kasuwar Mile 12 International Market da ke jihar Lagas, yayin da a makon da ya gabata aka sai da ₦220,000, an samu ragin ₦20,000 a makon nan da ke dab da ƙarewa.
A kasuwannin jihar Adamawa ana sai da buhun wake ₦170,180,-190,000 a satin nan, haka aka sai da satin da ya shuɗe.
To a jihohin Kano da Kaduna da ma Katsina, ana sayar da buhun wake ₦170,000 a wannan mako, farashin haka yake a makon da ya gabata a kasuwannin jihohin Kaduna da Katsina, sai dai kuma a jihar Kano farashin waken ₦155,000 ne a makon da ya gabata.
Bari mu kammala farashin kayan abinci na wannan sati da farashin taliyar Spaghetti.
Kwalin taliyar ya fi tsada a kasuwannin jihohin Kano da Kaduna da ake saidawa ₦19,500, bayan da a makon jiya aka sayar ₦18,000 a kasuwar Dawanau jihar Kano,sai Giwa jihar Kaduna aka sayar ₦19,000.
A kasuwar Mile 12 International Market Lagos ma farashin bai canza ba dana makon jiya, wanda aka sayar ₦19,000.
₦17,400 aka sayi kwalin taliya a kasuwar Mai’adua jihar Katsina a makon nan, bayan da a makon da ya shude aka saya ₦17,600.
To kasuwar zamani da ke jihar Adamawa ₦17,700 ake sayar da kwalinta a makon daya gabata, amma a makon nan ₦17,300 ne kuɗin kwalin taliyar.
Alƙaluman da hukumar kididdiga ta kasa ( NBS) ta fitar a watan Yulin 2024 ya nuna cewar hauhawar farashin kayayyakin masarufi ya yi kasa da kaso 33.40, saɓanin na watan Yuni da kaso 34.19.
DCL Hausa A’isha Usman Gebi.
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata